Maras Hoto
Search

Sangandale Rabonta Ya Rantse

14/06/2008
Saurari Kashin farko Na Hirar Sangandale Cikin Filin A Bari Ya Huce... - Download audio clip

Maryam A. Baba (Sangandale)
Maryam A. Baba (Sangandale)
Sunanta dai Maryam A. Baba, amma akasari idan mutum bai ce Sangandale ko kuma Maryam Sangandale ba, to zai yi wuya ma'abuta son wakokin zamani na Hausa su gane wadda ake fada. Daga lokacin da aka haife ta a Tal'udu a Unguwar Mai Nagge cikin birnin Kano, har ya zuwa wannan lokacin, Maryam Sangandale ba ta taba zaton za ta irin nasarar da ta samu a fagen wakoki ba.

Maryam A. Baba ta samo sunan Sangandale daga wata wakar da suka yi mai wannan suna tare da Misbahu M. Ahmed cikin fim din nan mai suna "Kansakali". Kamar yadda aka saba gani ga masu fina-finan Hausa da mawaka, irinsu Sa'adiyya Gyale (Sa'adiyya Mohammed) wannan sunan ya makale mata.

Kwanakin baya, Maryam Sangandale, wadda ita ma tana cikin kungiyar mawakan nan ta Sa'adu Zungur Entertainment Group, ta fito da faifanta na farko, wanda ba wakokin fim ba ne, mai suna "Hikima Taguwa" wanda a ciki ta rera wakoki irinsu "Rabo" "Samari" da makamantansu.

Wakarta mai suna "Rabo" ta janyo cacar-baki a saboda yadda wasu ke rade-radin cewa ta yi ne da wani babban jami'in gwamnatin Jihar Kano, har ma an hana saka wannan waka a gidan rediyon Jihar Kano. Ina gaskiyar wannan magana?

A cikin hirar da ta yi da filin "A Bari Ya Huce..." Maryam Sangandale ta tattauna kan wannan batu na wakar "Rabo" har ma da yadda ta faro waka da cikakken tarihin rayuwarta, da kuma yadda take harhada wakoki ko fito da karinsu.

Idan ana son jin wannan hira cikin filin A Bari Ya Huce sai a matsa rubutun dake saman wannan labarin.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Labarai Masu Alaka
Wakokin Aminu Ladan Abubakar, Alan Waka, Su Na Yin Kasuwa Sosai
 
  Muhimmin Labari
Yau Laraba  taron Jam・iyyar Republican zata ayyana tsaida dan takarar shugaban kasa John McCain,da matai makiyar sa Sarah Palin.

  Karin Labarai
Yau Talata Jam・iyyar Republican ta Amurka zata fara aiwatar da shirye shiryen taron ta na kasa gadan gadan
Ruwa na pantsama ya tsallaka  manyan katangu da aka gina a New Orleans
Barack Obama ya anshi zabin da jamiyyar sa ta democrat tayi masa na zama dan takarar shugaban kasa
A yammacin Alhamis din nan ne, dan takarar shugabancin Amurka na Jam・iyyar Democrat, Barack Obama,zaiyi na・am da tsaida shi dan takara
Hillary Clinton ta kirayi illahirin .Yan .Jam・iyyar Democrat, su marawa Obama
Michelle Obama, matar dan takaran jam・iyyar Democrat, ta  gayawa mahalarta taron cewa Obama zai zamar wa Amurka hazikin shugaba
Yau litinin dinnan abude babban taron Jam・iyyar Democrat a Denver, jihar Colorado
A daren yau Laraba  taron Jam・iyyar Republican zata ayyana tsaida dan takarar shugaban kasa John McCain,da matai makiyar sa Sarah Palin.
Tsohon firayim ministan kasar Pakistan ,Nawaz Sharif, ya yanke sabon lokacin dawo da manyan alkalan kasar
Jam・iyyar Democrat ta Amurka, a makon gobe, zatayi taron ta na kasa a Denver,Colorado.
Masana Kimiyya Sun Gano Kaburburan Mutanen Zamanin Da Cikin Hamadar Sahara A Nijar
Gasar Kacici-Kacici Ta 2008
Wani Maganin Tarin Fuka Yana Rage Karfin Maganin Kashe Kaifin Cutar Kanjamau
Yau Litinin Jacob Zuma Zai Bayyana Gaban Kotu A Afirka Ta Kudu
Steve Lucas Yayi Ban Kwana Da Muryar Amurka  Audio Clip Available
Hukumomin Kasar Chile Sun Sa Idanu Kan Wasu Duwatsu Biyu Masu Aman Wuta