Jam'iyyar
Democrat ta Amurka, a makon gobe, zatayi
taron ta na kasa a Denver,Colorado. Za a fara taron, daga 25 zuwa 28,
na watan
Agusta, 2008.
A
lokacin taron ne Jam'iyyar Democrat ta Kasa,zata tsaida
Senata Barack Obama,takarar shugabancin Amurka.
Fitattun
mutane da dama ne zasu yi jawabai a taron na kwana
hudu. A jerin farko na masu yin jawabai,
har da babbar abokiyar hamayyar sa, a
zazzafar yakin share fagen tsaida dan takara na Jam'iyyar,Senata
Hillary
Clinton,da mai gidanta,tsohon shugaban kasa Bill Clinton.
Haka kuma a
yini na
farkon, Michelle Obama,uwargidan senata Obama,kakakin Majalisa Nancy
Pelosi,da
kuma tsohon shugaban kasa Jimmy Carter,suna cikin masu gabatar da
jawabai.
Taken jawaban wannan yini, shine:Kasa Daya,Al'uma Daya.