Barack Obama ya anshi zabin
da jamiyyar sa ta democrat tayi masa na zama dan takarar shugaban kasa,wanda
yayi fice a tarihi, kuma ya shiga yakin neman zaben shugaban kasa na tsawon
wata biyu a matsayin bakar-fatar Amurka na farko da rike tutar shugabancin babbar jamiyya.
Sanata Obama da abokin
takarar sa ,Sanata Joe Biden,a yau juma'a zasu tafi jahar Pennsylvania,dake
arewacin Amurka akan bos da zai yawata da su manyan jahohi.
A daren alhamis, Obama ya
bayyana gaban jama'a fiye da dubu tamanin,suna masa tafi da shewa,inda yayi
alkawarin kawo canji a kasar Amurka ya kuma bayyana banbancin sa da dan
hamayyar sa na jamiyyar republican,Sanata John Mccain.