Ruwa
na pantsama ya tsallaka manyan katangu
da aka gina a New Orleans,duk da haka shugabanni sun hakikance ba zasu rushe
ba,duk da farmakin da mummunar guguwar tekun mai karfin gaske (Gustav) take
kawowa.
Guguwar bata dira kai tsaye kan birnin New Orleans yau litinin,ta sauka
doron kasa da nisan kilomita 110 kudu maso yammacin New Orleans. Guguwar Gustav
ta isa doron kasa a rukuni na biyu da iska dake gudun kilomita 175 cikin ko wace
sa'a daya.
 |
| New Orleans evacuee Nathan Robichaux along with his daughter, Natalie, wait outside of a shelter in Theodore, Alabama, 01 Sep 2008 |
Ana sa ran zata fatattaki birnin na sa'o'I masu yawa. Hukumomi sunce
kamar kashi 95 cikin dari na mazauna yankin da iskar takewa barazana sun kwashe
na su ye nasu sun tsere,saboda tuna irin barnar da wata guguwar Katrina ta yi a
wannan yankin shekaru uku da suka wuce. Katrina ta rusa ganuwar tare ruwa, da
aka gina,sakamakon haka kashi 80 cikin dari na birnin ya cike daruwa.