Jam'iyyar
Republican ta Amurka zata fara aiwatar da shirye shiryen taron ta na kasa gadan
gadan ,bayan da guguwar teku mai karfi ta(Gustav) ta sanya Jam'iyyar takaita shirye
shiryen ta a yinin farko jiya litinin.
Kamfanonin dillancin labaru sun bada labarin watakil shugaba Bush zai yi
jawabi ga gangamin daga Fadar white House ta tauraruwar dan Adam.Ya soke
halartar taron jiya litinin domin ya maida hankali wajen ganin yadda Gwamnatin
tarayya take tafiyar da ayyukan agazawa yankin da guguwar Gustav ta rutsa.
 |
Cindy McCain (l) tare da Laura Bush
|
Tsohon magajin garin N/Y Rudy Gulianai,wadda shima yayi takarar neman a tsaida
shi shugabancin Amurka karkashin Jam'iyyar ta Republican zai gabatar da jawabi
na musamman ga gangamin a yau Talata.
John Mccain,wadda cikin makon nan ne zai
yi jawabin amincewa da tsaida shi takarara,jiya litinin ya wuni ne a Jihar Ohio
dake tsakiya maso yammacin Amurka inda ya maida hankali kan guguwar Gustav
wacce ta fatattaki yankuna dake dab da gaba. Uwargidan John Mccain,tareda
uwargidan shugaba Bush Laura, sunyi jawabai ga takaitaccen taron inda suka bukaci mahalarta su jingine
siyasa su bada gudumawa ga ayyukan jinkai.