Sakatare
Janar na majalisar Dinkin Duniya, Ba Ki-moon zai sauka a birnin Nairobin Kenya
a yau Juma¡Ša, domin halartar wani taro da zai tattauna matsalar Jamhuriyar
Kwango ta Kinshasa.
Ana sa ran
Shugaban Kwango, Joseph Kabila zai halarci taron, tare da takwaransa na Rwanda
Paul Kagame, da wasu shugabannin kasashen Afirka biyar.
Jami¡Šar
Diplomasiyyar Amurka, Jendayi Frazier wata kwararriya a kan harkokin Afirka,
ita ce zata wakilci Amurka a wajen taron.
A jiya
Alhamis Ban Ki-moon yayi kiran da a gaggauta tsagaita wuta a fadan da ake
fafatawa a gabashin kasar tsakanin dakarun gwamnati da ¡¥yan tawaye, wanda yayi
sanadiyyar mutuwar dubban mutane.
Wata
kungiyar kare hakkin dan adam, Human Rights Watch ta fada a jiya Alhamis, cewa
an kashe mutum 20, a yakin da suke domin kame kauyen Kiwanja. Kungiyar tace
dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisr Dinkin Duniya in banda kallo babu abin
da suke tabukawa.