Babbar kungiyar tsagerun yankin Niger Delta tana barazanar
haddasa mumunar fitina cikin yankin, idan ba ayi adalci kan batun tuhumar cin hanci da rashawa da akeyiwa
wasu jamiai cikin yankin.
Talata hukumar yaki da
masuyiwa tattalin arziki zagon kasa, EFCC, ta bada sanarwar kama babban jami¡¦in
kula da harkar mulki na Gwamnan Jihar Rivers,Nyeson Wike,da sakataren Gwamnatin
Jihar Magnus Abe, saboda zargin su da almubazzaranci.
Cikin sanarwa da kungiyar
MEND ta bayar yau Laraba,tace tana sa ido kan maganar sosai,saboda bata amincewa
Gwamnati ba,domin sai tayu a saki jami¡¦an ba tared anyi musu hukunci ba.
Kungiyar tace idan bata gamsu da yadda aka tafiyar da da batun ba,zata haddasa
mummunar rashin zaman lafiya a Jihar Rivers.