Maras Hoto
Search

Sudan Ta Bada Sanarwar Tsagaita Wuta A Yankin Darfur

12/11/2008

 

150_Darfur_Refugees_1Shugaban Sudan Omar al-Bashir, ya bada sanarwa shirin tsagaita wuta kai tsaye ba tareda wani sharadi ba, a arewcin kasar na yankin Darfur da yaki ya dai-dai ta.

Shugaban yayi kira yau da akawo karshen fada tsakanin sassa dake gaba da juna,kuma  a girke masu sa ido domin tabbatarda cewa duka sassan suna mutunta yarjejeniyar. Mr. Al-Bashir,yace Sudan zata bullo da shirin kwance damarar mayakan sakai,kuma ta takaita sojojinta  daga amfani da makamai. 

Jiya Talata wata kungiya da ake kira ta wanzarda Zaman lafiya da enci, ta bada shawarwarin samun zaman lafiya a yankin Darfur,da ya hada da shirin tsagaita wuta. Kungiyar ta kunshi ministoci da shugabanni daga Jam'iyun hamayya,kodashike 'yan tawayen yankin Darfur sun kaurace. Cikin shawarwari da kungiyar ta gabatar harda sakin fursinonin siyasa daga yankin Darfur,da kuma kirkiro mukamin mataimakin shugaban kasa domin yankin.

 

 

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Harin Isra'ila Ya Kasa Raunana Rokokin Hamas

  Karin Labarai
Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Zirin Gaza
Hukumomin Jihar Kano Sun Jefa Alhaji Hamisu Lamido Iyantama A Kurkuku  Audio Clip Available
John Atta-Mills Na Jam'iyyar Hamayya Ta NDC Shi Ne Sabon Shugaban Kasar Ghana
Isra'ila Ta Ce Lokacin Tsagaita Wuta Bai Zo Ba Tukuna
Shugaban Somaliya Yayi Murabus