Maras Hoto
Search

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi Tur Da Cin Zarafin 'Yan Hamayya Da Ake Yi A Zimbabwe

24/06/2008

Morgan TsvangiraiKwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yayi tur da tashin hankali da kuma cin zarafin da ake yi wa 'yan hamayyar siyasa na kasar Zimbabwe, yana mai fadin cewa ba zai yiwu a gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa tsakani da Allah cikin wannan yanayi a ranar jumma'a ba.

Ba tare da wata hamayya ba, dukkan wakilai 15 na Kwamitin Sulhun sun yarda da wata sanarwar da aka rage kaifin lafazinta wadda ta yi tur da farmakin da ake kaiwa kan 'yan hamayyar siyasar gwamnati kafin zagaye na biyu na zaben da za a yi.

Wannan shi ne karon farko da Kwamitin Sulhun MDD ya dauki wani mataki a kan rikicin kasar Zimbabwe.

Tun da fari a litinin, babban sakataren MDD, Ban Ki-moon, yayi kira ga Zimbabwe da ta jinkirta zaben na ranar jumma'a, yana mai fadin cewa duk wata kuri'ar da za a jefa a cikin wannan yanayi ba zata samu halalci ba.

Madugun hamayya, Morgan Tsvangirai, wanda tun farko ya gudu ya nemi mafaka a ofishin jakadancin kasar Netherland dake Harare, ya janye daga zagaye na biyu na zaben da za a yi tsakaninsa da shugaba Robert Mugabe, yana mai fadin cewa an kashe magoya bayan jam'iyyar hamayya masu yawa, wasu kuma an ji musu raunuka.

Jakadan Zimbabwe a MDD, Boniface Chidyausiku, yayi watsi da rahotannin tashin hankali, ya kuma ce za a gudanar da zaben ranar jumma'a kamar yadda aka shirya.

Jiya litinin, 'yan sanda sun kai sumame a hedkwatar jam'iyyar MDC ta Mr. Tsvangirai a Harare. Wani kakakin jam'iyyar ya ce 'yan sanda sun kama mutane kimanin sittin, akasarinsu mata da yara kanana. 'Yan sanda suka ce mutane talatin da tara suka kama.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Kamfanin Safarar Jirage Ruwa Mafi Girma A Duniya Yace Zai Kaucewa Mashigin Ruwan Aden.

  Karin Labarai
'Yan Bindiga A Yanmkin Niger Delta Sun Kaiwa Kamfanin Shell Hari.
Kungiyar al-Qaida Ta Yi Sako Ga Shugaban Amurka Mai Jiran Gado,Barack Obama.
'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Wani Gari A Somalia Dake Dab Da Kan Iyakarta Da Kenya.
Obama Da McCain Sunyi Alkwari Zasu Yi Aiki Tare.
Rilwan Lukman Yana Cikin Jerin Sunayen Mutane Goma Sha Uku Da Shugaban Najeriya Ya Gabatarwa Majalisar Dattjiai Domin A Nadasu Ministoci.
Hukumar Kiyaye Hakkin Bi'adama Ta Majalisar Dinkin Duniya Tana Kira Ga Isra'ila Ta Janye Kawanya Datakeyiwa Zirin Gaza
India Ta Nutsar Da Jirgin 'Yan Fashin Jirage A Somalia
Shugaban Kwango Laurent Kabila Ya Kori Babban Hafsan Mayakan Kasar,Dakarunsa Suna Ci Gaba Da Shan Kashi A Hanun 'Yan Tawaye.
Shugabannin Kamfanonin Kera Motoci A Amurka, Zasu Bayyana A Gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Amurka.
Babban Jirgin Ruwa Dake Dakon Mai Da Aka Sace Ya Kusa Isa Gabar Ruwan Somalia
Iraq Ta Yarda Amurka Taci Gaba Da Kasancewa Cikin Kasar Har Zuwa 2011.
'Yan Bindiga Sun Yi Fashin Wani Jirgin Dakon Kaya A Yankin Niger Deltan Najeriya
'Yan Tawaye A Kwango Sun Sake Kwace Wasu Sabbin Yankuna,A Dai Dai Lokacinda Shugabansu,Lauren Nkunda Ya Gana Da Manzon Majalisar Dinkin Duniya,Janar Obasanjo.
A Yau Litinin,Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Barack Obama,Yana Ganawa Da Abokin Hamayyarsa A Zaben Shugaban Kasa, John McCain.
Turai Tace Kasashenda Ke Cikin Kungiyar MAsu Aiki Da Kudin Euro Suna Fuskantar Koma Bayan Tattalin Arziki
Pakistan Tana Zargin AMurka Ta Kai Hari Da Makamai Masu Linzami A Yankin Kasar.
Jam'iyyar 'Yan Hamayya MDC A Zimbabwe Tana Taron Koli Domin Tsaida Shawarar Ko Ta Shiga Gwamnatin Hada Kan Kasa
Senata Hillary Clinton Ce Obama Zai Zaba Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka?
An Takaita Ikon Bin Laden A Alkaida
Shugaban Amurka mai Jiran Gado Barack Obama,zai Maye Gurbin Wasu Manyan Jami'an Ayyukan Lelen Asiri Biyu Cikin Watan Janairu
Majalisar Dinkin Duniya Tana Nazarin Bukatar Tura Karin Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya A Kwango
'Yan Bindiga Sun Harbe Wani Ba Amerike  Da Matukinsa Har Lahira A Peshwar.
Sudan Ta Bada Sanarwar Tsagaita Wuta A Yankin Darfur
Shugabannin Amurka Mai Barin Gado George Bush,da Magajinsa Barack Obama, Sun Gana A Fadar White House Jiya Litinin
Hannayen Jari A Kasuwannin Turai da Asiya Sun Yi Kasa A Hada-Hadar Yinin Talata
Wata Kungiyarda Gwamnatin Sudan Ta Kafa Tana Kira Da Tsagaiata Wuta A Fafatawarda Akeyi A Yankin Darfur
Yau Ce Cikar Shekaru 90 Da Kammala Yakin Duniya Na Daya
Miriam Makeba Ta Rasu
Bam Ya Kashe Akalla Mutane Ashirin Da Takwas A Bagadaza
Shugaban Amurka Mai Barin Gado GeorgeBush ,Zai Karbi Bakuncin Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Barack Obama A Fadar White House.
Shugabannin Siyasar Ivory Coast Sun Fara Taro Domin Tattaunawa Kan  makomar Zaben Kasar Da Ake Yawan Jinkirtawa
Shugaban Amurka Mai Jiran Gado,Barack Obama,Ya Yi Taronsa Farko Da Manema Labaru Tun Bayan Samun Nasara Zabensa
Ban Ki-moon Zai Ziyarci Kwango
Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Ya Gana Da Masu Bashi Shawara Kan Harkokin Tattalin Arziki
Obama Ya Fara Tunkarar Tattalin Arziki
Asusun Bada Lamuni(IMF),Yace Tattalin Arzikin Kasashe Da Dama Suna Fuskantar Barazana
Ana Sa Ran Sabon Zababben Shugaban Kasar Amurka Barack Obama Zai Bayyana Sunayen Wasu Manyan Jami'an Gwamnatinsa Bada Jumawa Ba.