Shugaban
Amurka mai jiran gado Barack Obama,da abokin hamayyarsa a zaben shugaban
kasa,John McCain,sun yi alkawarin zasu yi aiki tare kan matsalar tattalin
arziki,da wasu manyan matsaloli da Amurka take fuskanta.
A jiya litinin,Mr.
Obama ya gana fuska da fuska da Mr. McCain,a karo na farko tun kada Senatan
daga Jihar Arizona, a zaben shugaban kasa da aka yi ranar 4 ga watan Nuwamban
nan.
A sanarwar hadin gwiwa da mutanen
biyu suka bayar,sunce sun gudanar da tattaunawa mai armashi kan bukatar
kaddamar da sauyi.Haka kuma sun ce akwai bukata daukan matakin bai daya domin
rage yawan barnar da ake yi a Gwamnati da mummunar hamayya a Washington da
nufin sake farfado da amincewar da ”„yan kasa sukayiwa Gwamnati,da sake dawo da bunkasa, da yelwa ga dumbin
Amurkawa masu kuzarin aiki.