VOANews.com

 

Yau A VOA:

Labarai Cikin Harsuna 45
Shugaban Kwango Laurent Kabila Ya Kori Babban Hafsan Mayakan Kasar,Dakarunsa Suna Ci Gaba Da Shan Kashi A Hanun 'Yan Tawaye.

18/11/2008

 

Congolese soldiers march from Kibati, north of the provincial capital of Goma, as civilians flee the area, 7 Nov. 2008Shugaba Joseph Kabila, na Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango,ya maye gurbin shugaban rundunar mayakan kasar,yayin da dakarunsa suke ci gaba da fama kan 'yan tawaye dake ci gaba da dannowa a wani lardin kasar dake gabashi. 

A yammacin jiya Litinin ce,shugaba Kabila ya kori Lt.Janar Dieudonne Kayemba,ya maye gurbinsa da Lt.Janar Didier Etuma.  Gidan radiyo da Majalisar Dinkin Duniya yake gudanarwa da ake kira Okapi,yace sabon hafsan mai shekaru 53 da haifuwa,ya sami horon soji a Brussels,kuma ya taba rike mukamin babban hafsa mai kula da harkar mulki na sojojin ruwan Kwango. Dakarun Gwamnatin kasar suna shan kashi a hannun 'yan tawayen dake karkashin bijirarren janar Laurent Nkunda,tun sa'adda 'yan tawayen suka kaddamar da farmaki a lardin Kivu ta Arewa cikin watan jiya. 

Yau Talata,sojojin Gwamnati sun kara da mayakan sa kai kusa da garin Kanyabayonga. Madugun mayakan sa kai Sikuli Lafontaine, ya gayawa manema labaru cewa Dakarun sun kai hari kan mazauna kauyuka,suka kwashi ganima,bayan arangamar da suka yi  dasu.

 

 


E-mail This Article Aika Labarin Nan ma Wani Ta E-Mail
Print This Article Shafi Mai Saukin Bugawa
  Muhimmin Labari
Harin Isra'ila Ya Kasa Raunana Rokokin Hamas

  Karin Labarai
Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Zirin Gaza
Hukumomin Jihar Kano Sun Jefa Alhaji Hamisu Lamido Iyantama A Kurkuku  Audio Clip Available
John Atta-Mills Na Jam'iyyar Hamayya Ta NDC Shi Ne Sabon Shugaban Kasar Ghana
Isra'ila Ta Ce Lokacin Tsagaita Wuta Bai Zo Ba Tukuna
Shugaban Somaliya Yayi Murabus