VOANews.com

 

Yau A VOA:

Labarai Cikin Harsuna 45
Shugabannin Kamfanonin Kera Motoci A Amurka, Zasu Bayyana A Gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Amurka.

18/11/2008

 

New fuel standards will prevent release of carbon dioxide emissions of nearly 2.3 million automobilesYau Talata shugabannin kamfanonin kera motocin Amurka zasu bayyana gaban Majalisar Dokoki,domin neman tallafi ga masana'antun dake fama da matsaloli. 

Shugabannin kamfanonin General Motors, da Ford da Chrysler, tare da shugaban kungiyar ma'aikata dake yiwa kamfanonin aiki duk za su bada shaida gaban kwamitin majalisar Dattijai dake nazarin matsalar masana'antun ke fuskanta.  

Wakilan Democrat a Majalisar suna goyon bayan ayi amfani da dala miliyan dubu ashirin da biyar daga kudade da aka ware domin ceto bangaren kudi domin tallafawa masu kera motocin.Amma gwamnatin Bush tace kuskure ne a baiwa kamfanonin kudaden ba tare da sunyi garambawul ta yadda za su ci riba ba.

Gwamnatin ta Bush tana bada shawarar kamfanonin kera motocin su  sake tsara abinda ke hanunsu ta wajen amfani da rance da aka basu a baya ta hannun Ma'aikatar makamashi.

 


E-mail This Article Aika Labarin Nan ma Wani Ta E-Mail
Print This Article Shafi Mai Saukin Bugawa
  Muhimmin Labari
Harin Isra'ila Ya Kasa Raunana Rokokin Hamas

  Karin Labarai
Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Zirin Gaza
Hukumomin Jihar Kano Sun Jefa Alhaji Hamisu Lamido Iyantama A Kurkuku  Audio Clip Available
John Atta-Mills Na Jam'iyyar Hamayya Ta NDC Shi Ne Sabon Shugaban Kasar Ghana
Isra'ila Ta Ce Lokacin Tsagaita Wuta Bai Zo Ba Tukuna
Shugaban Somaliya Yayi Murabus