A daren yau Laraba ce wakilai dake halartar babban taron
Jam'iyyar Republican zasu ayyana tsaida mai yiwa Jam'iyyar takarar shugaban
kasa John McCain,da matai makiyar sa Sarah Palin.
Ana sa ran Palin zata yi na'am da tsaidata 'yar takara a wani
jawabi da ake dokin sa a muhimmin lokaci da Amurkawa ke maida hankali ga
talabijin a daren na yau,domin gabatar da ita garesu. McCain da mai dafa masa
baya sun sami dumbin goyon baya daga fitattun magoya baya,ciki har da shugaba
George Bush, a taron Jam'iyyar na jiya da dare. 
Da yake magana ta taurawurar
dan'adama daga Fadar White House,Mr. Bush yace Mccain ya san hanyoyin kare
Amurka daga harin masu kisa ta'addanci.Ya kuma yaba masa saboda goyon bayan da
McCain ya bayar ga shirin tura karin
sojoji Iraqi.