Makeken Jirgin Dakon Mai na Saudiyya dauke da
Mai da kudinsa ya kama dala miliyan dari,da aka sace ya kusa isa gabar ruwan tekun Somaliya.
Mai Jirgin
ruwan da aka sace'Sirius Star', yace babu daya daga cikin ma'aikatan jirgin su-
ashirin da biyar da aka jikkata. Asabar ce 'Yan fashin jirgin ruwa daga Somalia
cikin kananan jirage masu dan Karen gudu
suka kama makeken jirgin ruwan dake nisan kilomita 800 daga gabar
Kenya,nesa daga inda barayin suka saba yiwa jiragen kwanton bauna.
Shugaban
hafsan hafsoshin Amurka Admiral Mullen, yace ya yi mamakin irin nisan gudun da
'yan fashin jirgin ruwan suke kaiwa wajen aika aikarda suke yi. Jirgin wadda
Tankin Mai ne yana dauke da gangar mai milyan biyu,kuma an sace shi duk da
kasancewar hadin gwiwar jiragen yaki na kasa da kasa a ruwayen Somalia domin
hana irin wannan fashin.Jiragen yakin sun hada da na kungiyar Tsaro Ta NATO da
kuma na mayakan ruwan Amurka.
Ministan
harkokin wajen Saudiyya Yerima Saud al-Faisal,yau Talata, yace fashin abin
bakin cikine. Yace fashi cikin ruwa tamkar ta'addanci ne,ya kira shi cuta wacce
tilas kowa ya yake ta.