Yau
ake sa ran yin muhawarar farko tsakanin 'yan takarar shugabancin Amurka Barack
Obama,da abokin karawar sa na Republican John
McCain,bayan da shi McCain ya jingine yakin neman zaben sa.
Wakilan
Democrats suna zargin John McCain da
laifin rugujewar yarjejeniyar dala bilyan dari bakwai na ceto cibiyoyin
kudi,bayan shawarwari da akayi a fadar White House jiya Alhamis. Senata Chris
Dodd,shugaban kwamitin harkokin Bankuna a majalisar Dattijai,yace taron 'Shirin
ceto John Mccain ne". 
Shi ma Obama ya
zargi McCain da cusa siyasar yakin neman shugabancin Amurka cikin shawarwarin
ceto cibiyoyin kudin.